Somaliya : Sabon Babban Hafsan Soji Ya Tsallake Rijiya Da Baya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19286-somaliya_sabon_babban_hafsan_soji_ya_tsallake_rijiya_da_baya
Rahotanni daga Somaliya na cewa babban hafsan sojin kasar da aka nada kwanan nan, ya tsallake rijiya da baya, sakamakon yadda wani harin bom da mota ya so ritsawa dashi a Mogadisho babban birnin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:56+00:00 )
Apr 09, 2017 11:05 UTC
  • Al'shabab ta dauki alhakin kai harin.  HOTO : AFP
    Al'shabab ta dauki alhakin kai harin. HOTO : AFP

Rahotanni daga Somaliya na cewa babban hafsan sojin kasar da aka nada kwanan nan, ya tsallake rijiya da baya, sakamakon yadda wani harin bom da mota ya so ritsawa dashi a Mogadisho babban birnin kasar.

Bayanai daga kasar sun ce wani direba da mota shake da boma boma ya aukawa ayarin motocin sabon babban hafsan sojin kasar Mohamed Jama Irfid a wannan Lahadin.

Wata majiya tsaro ta shaidawa kamfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa tawagar babban hafsan duk sun kubuta da harin.

Lamarin dai ya auku ne a kusa da ma'aikatar tsaron kasar inda aka samu rahotannin mutuwar fararen hula hudu da kuma wani soja guda.

kungiyar Al'shabab ta dauki alhakin kai harin ta gidan radiyon ta na Andalus jim kadan bayan aukuwar lamarin.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan ikirarin shugaban kasar ta Somaliya Mohamed Abdullahi Mohamed na baiwa kungiyar ta Al'shabab wa'adin kwanaki 60 su mika wuya ko kuma su kuka da abunda zai biyo baya.