Masar : IS Ta Dauki Alhakin Harin Da Ya Kashe Mutane 43
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19294-masar_is_ta_dauki_alhakin_harin_da_ya_kashe_mutane_43
Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta dauki alhakin kai hare-haren da sukayi sanadanin mutuwar mutane akalla 43 a wasu majami'i biyu na Masar a wannan safiyar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 09, 2017 12:52 UTC
  • Harin na zuwa ne a kasa da kwanaki 19 da ziyara Paparoma Fransis
    Harin na zuwa ne a kasa da kwanaki 19 da ziyara Paparoma Fransis

Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh ta dauki alhakin kai hare-haren da sukayi sanadanin mutuwar mutane akalla 43 a wasu majami'i biyu na Masar a wannan safiyar.

An kai harin ne lokacin da Kiristoci Kifdawa ke bikin Palm Sunday, daya daga cikin ranaku mafiya tsarki a addinin Kirista, domin tunawa da galabar da Almasihu ya samu ta sake shiga birnin Qudus.

Harin mafi muni shi ne wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 27 tare da raunana wasu 78 a cocin kifdawa ta birnin Tanta, sai kuma na cocin Alexandri da ya hallaka mutane 16 da raunana wani adadi mai yawa.

Wadanne hare-haren na zuwa ne a kasa da kwanaki 19 kafin ziyara da ake sa ran Paparoma Faransis na mabiya darikar Katolika zai soma a kasar ta Masar daga ranar 28 na watan nan.

Gwamnatin Masar dai ta bakin firaministanta  Cherif Ismaïl ta yi Allah wadai da hare-haren tana mai kara jadadda ci gaba da yakar ayyukan ta'addanci tun daga tushensu.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba a ake kai hari makamancin hakan a wannan kasar ta Masar ba inda ko a watan Disamba bara wani makamacinsa ya yi sanadin mutuwar mutane 29 a mujami'un Saint-Pierre da kuma Saint-Paul dake Alkahira babban birnin kasar.