Bullar Cutar Kwalara Ta Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan Ta Kudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19312-bullar_cutar_kwalara_ta_lashe_rayukan_mutane_a_kasar_sudan_ta_kudu
Ma'aikatar lafiya a Sudan ta Kudu ta sanar da mutuwar mutane akalla 29 sakamakon bullar cutar kwalara a kasar
(last modified 2018-08-22T11:29:56+00:00 )
Apr 10, 2017 12:00 UTC
  • Bullar Cutar Kwalara Ta Lashe Rayukan Mutane A Kasar Sudan Ta Kudu

Ma'aikatar lafiya a Sudan ta Kudu ta sanar da mutuwar mutane akalla 29 sakamakon bullar cutar kwalara a kasar

Ma'aikatar lafiya a Sudan ta Kudu ta sanar da cewa tun bayan bullar cutar kwalara a kasar a watan Fabrairun wannan shekara; a halin yanzu haka akwai mutane fiye da 200 da suka kamu da cutar, kuma akalla 29 ne daga cikinsu suka mutu.

Ma'aikatar lafiyar ta kara da cewa: Mafi yawan mutanen da suka kamu da cutar sun fito ne daga yankunan tekun Nile sakamakon matsalar da suke fama da ita ta rashin tsabtaceccen ruwan sha gami da karancin kayayyakin kiwon lafiya.