An Hallaka 'Yan Ta'adda Da Dama a Kudancin Masar
Ma'aikatar cikin gidan Masar ta sanar da hallakar 'yan ta'addar ISIS 7 a kudancin kasar
Cikin Wani jawabi da ta fitar a daren jiya Litinin, Ma'aikatar cikin gidan Masar ta ce Dakarun tsaron kasar sun kai farmaki a maboyar 'yan ta'adda a garin Anbub dake cikin jihar Esyout tare da samun nasarar hallaka 'yan ta'adda masu alaka da kungiyar ISIS 7.
Sanarwar ta ce 'yan ta'adda ne suka shirya harin da aka kaiwa mabiya addinin kirista a majami'ar su da kuma wasu hare-haren da aka kai a wasu cibiyoyin tsaro, tattalin arziki da kuma filayen wassani a kasar.
Wannan farmaki na Dakarun tsaron kasar Masar na zuwa ne kwana guda kacal bayan harin ta'addancin da aka kai kan wasu Majami'u na Kifdawa a gariruwan Tanta da kuma Eskandariya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla Mutane 45 tare da jikkatar wasu 125 na daban.
Kungiyar ISIS dai ta dauki alhakin kai harin na ranar Lahadin da ta gabata, tare da yin barazanar ci gaba da kai irin wadannan hare-haren ta'addanci nan gaba a kasar ta Masar.