Sojojin Kenya Sun Kashe 'Yan Ta'addan Al-Shabab Na Somaliya Masu Yawa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19340-sojojin_kenya_sun_kashe_'yan_ta'addan_al_shabab_na_somaliya_masu_yawa
Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Kenya da kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na Somaliya ya lashe rayukan 'yan ta'adda akalla 15 tare da jikkatan wasu adadi na daban.
(last modified 2018-11-18T05:33:40+00:00 )
Apr 11, 2017 05:38 UTC
  • Sojojin Kenya Sun Kashe 'Yan Ta'addan Al-Shabab Na Somaliya Masu Yawa

Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Kenya da kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab na Somaliya ya lashe rayukan 'yan ta'adda akalla 15 tare da jikkatan wasu adadi na daban.

Kakakin rundunar tsaron Kenya Joseph Utte a cikin daren jiya wayewar garin yau Talata ya sanar da cewa: Sojojin gwamnatin Kenya sun yi dauki ba dadi da mayakan kungiyar ta'addanci ta Al-Shabab a yankin Kutama na Kenya da ke makobtaka ta yankin Geidu na kasar Somaliya, inda sojojin Kenya suka yi nasarar kashe 'yan ta'adda akalla 15 tare da jikkata wasu da dama. 

Kakakin rundunar tsaron kasar ta Kenya ya kara da cewa: Sojojin Kenya karkashin jagorancin dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na "AMISON" zasu ci gaba da kaddamar da hare-hare kan 'yan kungiyar ta Al-Shabab da nufin karya lagonsu.