Najeriya: 'Yan Bindiga Sun Sace Turkawa Biyu A Jihar Akwa-Ibon
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19350-najeriya_'yan_bindiga_sun_sace_turkawa_biyu_a_jihar_akwa_ibon
Majiyar yansanda a tarayyar Nigeria ta bayyana cewa wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba'a tantance ko su waye ne ba sun sace mutane biyu yan kasar turkia a wani hotel da suke zama a birnin Ikiti na Jihar Akwa-Ibon daga kudancin kasar.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 11, 2017 14:32 UTC
  • Najeriya: 'Yan Bindiga Sun Sace Turkawa Biyu A Jihar Akwa-Ibon

Majiyar yansanda a tarayyar Nigeria ta bayyana cewa wasu yan bindiga wadanda har yanzun ba'a tantance ko su waye ne ba sun sace mutane biyu yan kasar turkia a wani hotel da suke zama a birnin Ikiti na Jihar Akwa-Ibon daga kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya ce mutanen biyu suna aikiwa wani kamfanin gine gine a garin Onna na jihar ta Akwa Ibon kuma har ya zuwa lokacin bada wannan labarin ba wanda ya dauki nauyin sace su ko kuma da wani dalili ne aka sace su.

Satar mutane don karban kudaden fansa, musamman yan kasashen waje ya zama ruwan dare a tarayyar Nigeria musamman kuma  daga yankin Niger Deltar mai arzikin man fetur.