Gwamnatin Sudan Ta Tabbatar Da Halakar Sojojinta 5 A Yemen
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19362-gwamnatin_sudan_ta_tabbatar_da_halakar_sojojinta_5_a_yemen
Gwamnatin kasar Sudan ta tabbatar da halakar 5 daga cikin sojojinta da ke wa Saudiyya yaki a kasar Yemen, bayan da dakarun Yemen tare da sojojin sa kai na kabilun kasar suka rutsa da su a kan iyakokin kasar ta Yemen da Saudiyyah a cikin gundumar Sa'adah.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Apr 12, 2017 01:50 UTC
  • Gwamnatin Sudan Ta Tabbatar Da Halakar Sojojinta 5 A Yemen

Gwamnatin kasar Sudan ta tabbatar da halakar 5 daga cikin sojojinta da ke wa Saudiyya yaki a kasar Yemen, bayan da dakarun Yemen tare da sojojin sa kai na kabilun kasar suka rutsa da su a kan iyakokin kasar ta Yemen da Saudiyyah a cikin gundumar Sa'adah.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, dakarun Yemen tare da sauran sojin sa kai na kabilun larabawan Yemen sun yi wa sojin Saudiyya tare da sauran sojojin haya kwanton bauna a arewacin kasar, inda suka kashe wasu daga cikinsu da suka hada har da sojojin haya daga Sudan, kamar yadda gwamnatin din ta tabbatar da hakan.

A cikin watan Fabrairun shekara ta 2016 da ta gabata ce masarautar Saudiyya ta saka kudaden ajiya a babban bankin kasar Sudan har dala biliyan1, bisa sharadin cewa Sudan za ta tura sojojinta domin yaki a kasar Yemen, sharadin da gwamnatin ta Sudan ta amince da shi, inda a halin yanzu an kashe adadi mai yawa daga cikinsu.