Cutar Sankarau : Kimanin Mutane 500 Suka Mutu A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19388-cutar_sankarau_kimanin_mutane_500_suka_mutu_a_najeriya
Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta sanar da cewa kimanin mutane 500 ne kawo yanzu cutar sankarau ta kashe tun bayan bullarta a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:57+00:00 )
Apr 13, 2017 01:24 UTC
  • Cutar Sankarau : Kimanin Mutane 500 Suka Mutu A Najeriya

Ma'aikatar lafiya a Najeriya ta sanar da cewa kimanin mutane 500 ne kawo yanzu cutar sankarau ta kashe tun bayan bullarta a kasar.

Alkaluman wucin gadi da ma'aikatar ta fitar sun nuna cewa mutane 4,637 ne suka kamu da cutar a yayin da 489 suka rasu tun bayan bullarta a cikin watanni biyar din nan.

Da yake bayyana hakan a wani taron manema labarai a jiya Laraba, ministan kiwan lafiya al'umma na kasar, Osagie Ehanire ya ce cutar ta fi kamari a jihar Zamfara dake arewacin kasar wace keda kashi 70% na yawan wadanda suka kamu, inda kuma akayiwa mutane dubu 420 allura riga kafin cutar.

A karshen makon nan ne ake sa ran kasar za ta karpi wasu alluran roga kafin cutar dubu 823 daga kasar Burtaniya domin ci gaba da gudanar da gangamin yaki da cutar da aka kaddamar a ranar 5 ga watan Afrilun nan.

Saidai a cewar offishin yaki da cutukan dake zama annoba a kasar, jihar Zamfara a ita kadai na bukatar alluran riga kafin cutar kusan Miliyan uku.