Afrika Ta Tsakiya : Amurka Ta Kakabawa Jagororin Mayaka Takunkumi
Amurka ta sanar da kakabawa shugabanin mayakan dake rikici a jamhuriya Afrika ta tsakiya takunkubi saboda hannun da suke da shi a rkicin da kasar ta tsunduma.
Mutanen biyu wadanda takunkumin ya hau kansu sun hada da Abdulaye Hissene shugaban kungiyar Seleka ta galibi musulmi da kuma shugaban kungiyar Anti Balaka ta mabiya Krista, wato Maxime Mokom.
Amurkar dai ta sanar da toshe kaddarorin jagororin biyu .
A cikin sanarwar data fitar Amurka ta ce mutanen biyu na taka mahimiyyar rawa wajen kara rura wutar rikici a wannan kasa ta Afrika ta Tsakiya.
Kana kuma jagororin 'yan tawayen biyu sun kawo rudani wajen zaben jin ra'ayin al'ummar kasar da kuma hadassa cikas ga mulkin shugaba Faustin-Archange Touadera a cikin shekara 2016 data gabata.