Wasu 'Yan Bindiga Sun Harbe Jami'an 'Yan Sanda 8 A Tanzania
Wasu masu dauke da makamai sun harbe jami'an 'yan sanda 8 a gabashin kasar Tanzania.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, ofishin shugaban kasar Tanzania ya fitar da sanarwa a yau Juma'a da ke cewa, shugaba John Magufuli ya nuna matukar kaduwarsa, bayan samun labari a yau kan kisan da wasu 'yan bindiga suka yi wa jami'an 'yan sanda a gabashin kasar, yana mai isar da sakon ta'aziyya ga iyalan mamatan.
'Yan bindigar wadanda ba a san ko su wane ne ba, kuma ba a san manufarsu ba, sun harbe 'yan sanda ne a yankin Kebiti da ke gabashin birnin Darussalam, kuma suka tsere ba tare da an kame su ba.
Daga watan Oktoban da ya gabata ya zuwa, an kashe 'yan siyasa 9 daga jam'iyya mai mulki a wannan yanki, kamar yadda ko a cikin watan da ya gabata, an kashe jami'an 'yan sanda uku a yankin.