Shugaba Buhari Ya Kirayi 'Yan Nijeriya Da Su Kara Hakuri Da Gwamnatinsa
Shugaban Muhammadu Buhari na Nijeriya ya bukacin al'ummar kasar da su kara hakuri da gwamnatinsa da kuma yarda da karfin da take da shi na kawo sauyin da al'ummar suke bukata a kasar.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne cikin wani sakon bikin Easter da ya fitar inda ya ce gwamnatinsa tana nan daram din ta kan ci gaba da fada da ta'addanci da masu tada kayar baya, tabbatar da sulhu da zaman lafiya a yankin Niger Delta, tabbatar da sulhu da zaman lafiya a sauran yankuna na kasar da kuma fada da masu ta'annuti ga tattalin arzikin kasa.
Shugaban na Nijeriya ya bukaci 'yan kasar da su zauna lafiya da junansu da kuma kaunar bugu da kari kan sadaukarwa wajen ciyar da kasar gaba.
Shugaba Buhari ya taya Kiristocin Nijeriya din murnar bikin na Easter don tunawa da batun giciye Annabi Isa (a.s) da kuma lokacin da ya tashi.