Rikici Na Cilastawa Jami'an Agaji Ficewa Daga Sudan Ta Kudu
MDD ta sanar da cewa ana ci gaba da samun jami'an agaji dake ficewa daga yankunan dake fama da Rikice-rikice a Sudan ta kudu.
A ranar Litinin data gabata wasu jami'ai uku 'yan asalin Sudan ta kudun ne dake aiki karkashin wani kamfani a hukumar abinci ta duniya aka hallaka a yankin Wau dake arewa maso yammacin kasar.
Wannan dai a cewar MDD babban kalubale ne a yunkurin da ake da shi na isar da kayan agaji a wuraren dake fama da rikice-rikice a wannan kasar ta Sudan ta Kudu.
Dama kafin hakan jami'an agaji shida ne suka hallaka a wani harin kwatan bauna da aka kai masu a kan hanyar zuwa Juna da Pibor dake gabashin kasar.
Wannan al'amari dai ya sanya jami'an agaji ficewa daga yankuna da dama na Sudan ta kudun ciki har da Jonglei inda a yanzu haka aka rawaito jami'an agaji 60 wadanda suka fice daga kasar a Jiya Jumma'a.
Ofishin kula da ayyukan ji kai na MDD wato OCHA ya ce ya ji takaicin yadda wadanan abubuwan suke wakana kan jami'an agaji dake aikinsu na taimakawa mabukata.