Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Yankunan Kasar
(last modified Mon, 17 Apr 2017 05:48:56 GMT )
Apr 17, 2017 05:48 UTC
  • Jami'an Tsaron Masar Sun Kama Wasu Gungun 'Yan Ta'adda A Yankunan Kasar

Jami'an tsaron Masar sun yi nasarar kama wasu gungun 'yan ta'adda da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin gwamnati da wajajen bautan mabiya addinin Kirista a kasar.

Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Masar a jiya Lahadi ta fitar da bayanin cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar kama wasu gungun 'yan ta'adda na mutane 13 a lardunan Buhairah da Iskandariyya da suke shirye-shiryen kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan cibiyoyin gwamnati da wajajen bautar mabiya addinin Kirista, tare da gano rumbun makamai da suke amfani da su wajen kai hare-haren ta'addanci. 

A ranar 9 ga wannan wata na Aprilu ne dai aka kai wasu munanan hare-haren wuce gona da iri kan majami'un mabiya addinin Kirista a garuruwan Tanta da Iskandariyya da suke kasar ta Masar, inda hare-haren suka kashe mutane akalla 45 tare da jikkata wasu adadi masu yawa, kuma kungiyar ta'addanci ta Da'ish ta dauki alhakin kai hare-haren biyu.