Jana'izar Hassan al-Turabi A kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1954-jana'izar_hassan_al_turabi_a_kasar_sudan
Sudan: Jana'izar Hassan Turabi A Birnin Khartum
(last modified 2018-08-22T06:57:56+00:00 )
Mar 06, 2016 09:53 UTC
  • Jana'izar Hassan al-Turabi A kasar Sudan

Sudan: Jana'izar Hassan Turabi A Birnin Khartum

Kamfanin Dillancin Labarun (AFP) ya ambato cewa; Da safiyar yau lahadi ne aka yi jana'izar fitattacen dan siyasar Sudan mai ra'ayin musulunci Hassan Turabi wanda Allah ya yi wa rasuwa a jiya asabar.

Jana'izar Hassan Turabi ta sami halartar manyan jami'an gwamnati da dubban mutane. Daga cikin wadanda su ka halarci jana'izar tashi da akwai mataimakin shugaban kasar Sudan Bakry Hasan Salih da kuma wasu ministoci masu yawa da wakilan jam'iyyun siyasar kasar.

A jiya asabar ne dai Allah ya yi wa Hassan al Turabi rasuwa bayan gajeruwar jiyya ta ciwon zuciya.