NCAA: Gobe Laraba Za'a Bude Filin Jirgin Saman Abuja
Babban daraktan hukumar safarar jiragen sama ta Nijeriya (NCAA) Usman Muktar ya sanar da cewa an kammala ayyukan da ake yi a titunan sauka da tashin jiragen sama a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, don haka za a bude filin jirgin sama a gobe Laraba.
Mr. Muktar ya bayyana hakan ne a wata ganawa da yayi da manema labarai a lokacin da ya ce rangadi na karshe don duba titunan inda ya ce an gama dukkanin abin da ya kamata don haka za a iya bude filin jirgin sama a gobe Laraba don fara amfani da shi.
Shi ma a nasa bangaren Daraktan hukumar filayen jirgin sama na Tarayyar Nijeriya din (FAAN) Mraleh Dunoma ya ce an gama dukkanin ayyukan titunan don haka za a iya bude filin jirgin sama da aiki da shi.
A ranar 8 ga watan Maris din da ya gabata ne dai aka rufe filin jirgin na tsawon makonni shida don yin gyara ga titunan sauka da tashin filin jirgin sama.