Kungiyoyin Kasa Da Kasa Suna Goyon Bayan Gwamnatin Kasar Somaliya
Kungiyoyin Kasa da Kasa sun nuna goyon bayansu ga shirin gwamnatin Somaliya na magance matsalar farin da kasar ta ke fama da shi.
Kungiyoyin Kasa da Kasa sun nuna goyon bayansu ga shirin gwamnatin Somaliya na magance matsalar fari da kasar ta ke fama da shi.
Kamfanin dillancin labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato majalisar dinkin duniya, tarayyar turai, dakarun tarayyar Afirka a Somaliya, da kungiyar raya kasa ta yankin, Igad, a cikin wani bayani na hadin gwiwa suna bayyana gamsuwarsu da shirin tafiyar da siyasar kasar ta Somaliya, kamar yadda aka cimmawa a taron Magadishu.
Kungiyoyin sun kuma jaddada amincewarsu na taimakawa gwamnatin Somaliya wajen fuskantar fari da cin hanci da rashawa da kuma samo hanyoyin karuwar kudaden shiga.
Wakilin musamman na babban sakataren majalisar dinkin duniya, Micheal Kiting ya nuna gamsuwarsa da shirin.