Kungiyoyin Fararen Hula A Senegal Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Fursunoni Palastinawa
(last modified Wed, 19 Apr 2017 11:16:25 GMT )
Apr 19, 2017 11:16 UTC
  • Kungiyoyin Fararen Hula A Senegal Sun Nuna Goyon Bayansu Ga Fursunoni Palastinawa

Wasu manyan 'yan siyasa da kuma jami'an kungiyoyin fararen hula a kasar Senegal sun sanar da goyon bayansu ga fursunoni Palastinawa da suke tsare a gidajen yarin haramtacciyar kasar Isra'ila.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya bayyana cewar a wani zama da aka gudanar da ya sami halartar jakadan kasar Palastinu a Senegal Sawat Ibraghith da kuma wakilin kungiyar Amnesty International Seydi Gassama bugu da kari kan jami'an wasu kungiyoyin fararen hula na Senegal, mahalarta taron sun bayyana goyon bayansu ga fursunoni Palastinawa da kuma bukatar da a kyautata yanayin da suke ciki a gidajen yarin.

An gudanar da wannan taron ne dai don nuna goyon baya ga Palastinawa da suke tsare a gidajen yarin HKI, don tunawa da ranar 17 ga watan Aprilu da aka ba shi suna a matsayin ranar fursunoni Palastinawa.

Tun dai a shekaran jiyan dubun dubatan Palastinawan da suke tsare suka fara wani yajin cin abinci don tilasta wa sahyoniyawan kyautata musu yanayin da suke ciki.