Shugaban Kenya Ya Gargadi Masu Tayar Da Hatsaniya A Lokacin Zabe
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya yi gargadin shiga kafar wando daya da duk wanda ya nemi tayar da wata hatsaniya a lokacin gudanar da zabukan 'yan majalisa a kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a yau, shugaban kasar Kenya Uhuru enyatta ya bayyana cewa, ba zai iya jure wa tayar da duk wata tashin-tashina ba alokacin zaben 'yan majalisa mai zuwa, a kan haka za a dauki dukkanin matakai na doka domin tabbatar da cewa an yi komai bisa ka'ida.
A ranar 8 ga watan Agustan wanann shekara ta 2017 ce za a gudanar da zaben 'yan majalisar dokoki a kasar Kenya.
Kimanin mitane miliyan 19 ne daga cikin al'ummar kasar Kenya miliyan 45 suka cancanci kada kuri'a.