Shugaban Kasar Kenya Ya Gargadi Masu Son Kawo Cikas a Zaben Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19654-shugaban_kasar_kenya_ya_gargadi_masu_son_kawo_cikas_a_zaben_kasar
Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce zai saka kafar wando daya ga duk wanda aka samu da laifin kawo cikas a zaben kasar mai zuwa
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 21, 2017 01:05 UTC
  • Shugaban Kasar Kenya Ya Gargadi Masu Son Kawo Cikas a Zaben Kasar

Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya ce zai saka kafar wando daya ga duk wanda aka samu da laifin kawo cikas a zaben kasar mai zuwa

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya na cewa ba zai amince da duk wani mai son tada tarzoma a yayin zaben ba, kuma duk wanda aka samu da wannan laifi, za a gurfanar da shi a gaban Kuliya.

A ranar 8 ga watan Augustan 2017 ne za a gudanar da zaben Majalisa, bayan kwashe shekaru 10 ana fuskantar matsalar rikicin bayan zabe a kasar, zaben 'yan Majalisar da ya gabata ya fuskanci matsalar rikici yayin da 'yan adawa suka zargi Gwamnati da murguda sakamakon zabe, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane sama da dari.

A halin da ake ciki, tuni aka fara cacar baki tsakanin jam'iyun adawa da masu milki, wanda kuma hakan ne ma ya sanya Shugaban kasar yin wannan gargadi.

Kimanin 'yan kasar Kenya miliyan 19 ne suka caccanci kara kuri'a.