Sankarau Ya Kashe Mutane 120 A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19676-sankarau_ya_kashe_mutane_120_a_nijar
Wani rahoto da MDD ta fitar ya nuna cewa mutane 120 ne ciwan sankarau ya kashe a Jamhuriya Nijar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 21, 2017 12:34 UTC
  • Sankarau Ya Kashe Mutane 120 A Nijar

Wani rahoto da MDD ta fitar ya nuna cewa mutane 120 ne ciwan sankarau ya kashe a Jamhuriya Nijar.

Alkalumen da ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD a Nijar ya fitar ya ce mutane 2,102 ne suka kamu da cutar tun daga ranar 2 watan Janairu zuwa 19 ga watan Afrilu na shekara nan da muke ciki a duk fadin kasar.

Rahoton ya ce kashi 45% na mutanen da cutar ta fasha yara ne 'yan shekara biyar zuwa 14, kuma cutar ta shafi jihohin da suka hada da Yamai, Dosso, Tillabery da Tawa da kuma Maradi.

A ranar 13 ga watan Afrilun nan ma'aikatar lafiya ta kasar ta kaddamar da wani gagarimin kamfe na shaushawar yaki da cutar kuma za'a ci gaba da shirin har zuwa 24 ga watan.

Ma'aikatar lafiyar kasar dai ta ce tana da isasun zata iya yi ma mutane 25,000 magani.