Mauritania : Za'a Je Zaben Raba Gardama
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19678-mauritania_za'a_je_zaben_raba_gardama
A Mauritaniya za'a gudanar da zaben jin ra'ayin al'ummar a ranar 15 ga watan Yuli mai zuwa game da kudirin gwamnatin kasar na aiwatar da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 21, 2017 13:15 UTC
  • Mauritania : Za'a Je Zaben Raba Gardama

A Mauritaniya za'a gudanar da zaben jin ra'ayin al'ummar a ranar 15 ga watan Yuli mai zuwa game da kudirin gwamnatin kasar na aiwatar da wasu sauye-sauye a kundin tsarin mulkin kasar.

Sauye sauyen da gwamnatin ke son kawowa ga kudin tsarin mulkin kasar da ake aiki dashi tun shekara 1991,  ay shafi soke majalisar datijai da kuma canza tutar kasar.

Ko baya ga hakan dai kudirin na son a soke wasu mayan hukumomi na kasar ciki har da kotun koli da mukamin mai shiga tsakani na gwamanati da kuma majalisar koli ta Islama.

A ranar 9 ga watan Maris da ya gabata ne majalisar dokokin kasar ta amunce da shirin gwamnatin, sai dai majalisar datijan kasar tai watsi da shi kwanaki tara bayan da aka gabatar mata da shi don amuncewa.

Gamayar mayan jami'iiyun adawa na kasar dai sun soki matakin gwamnatin kasar na aiwatar da wannan gyran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.