Mutane 55 Sun Rasa Rayukansu A Rikicin Sudan Ta Kudu
Apr 22, 2017 17:38 UTC
Mahukuntan kasar Sudan ta kudu sun cewa akalla fararen hula 55 sun rasa rayukansu a rikicin da ake yi a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa ya bayar da rahoto daga birnin Juba cewa, a yau mahukuntan Sudan ta kudu sun ce wasu masu dauke da makamai sun kai hari a cikin jahar Buma da ke gabashin kasar, inda suka kashe mutane akalla 55 dtare da jikkata wasu.
Bayanin ya dora alhakin harin a kan mayakan 'yan tawaye da ke mara wa Reick Machar baya, to sai dai a nata bangaren majalisar dinkin duniya ta dora alhakin abin da yake faruwa a kasar a kan gwamnatin Slava Kiir.
Tags