Ziyarar Shugaban Kasar Masar A Saudiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19736-ziyarar_shugaban_kasar_masar_a_saudiya
Shugaban Kasar Masar ya fara Ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Saudiya
(last modified 2018-08-22T07:00:00+00:00 )
Apr 23, 2017 13:30 UTC
  • Ziyarar Shugaban Kasar Masar A Saudiya

Shugaban Kasar Masar ya fara Ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar Saudiya

Tashar Telbijin din Almayadeen ta kasar Labnon ta habarta cewa a wannan Lahadi, Shugaban kasar Masar Abdulfatah Alsese ya amsar goron gayyatar Shugaban kasar Saudiya Salman bn Abdul-Aziz da nufin farfado da alaka dake tsakanin buranen Riyad da Alkahira.

A cewar Alaae Yusuf mai magana da yawun fadar Shugaban kasar Masar, za a gudanar da zama tsakanin shugabanin kasashen Masar da Saudiya a yayin wannan ziyara, kuma kafin hakan, magabatan Saudiya sun yi alkawarin saka hanun jari na tsabar kudi biliyan 25 na dalar Amurka.

A nasa bangare Ministan harakokin wajen kasar Masar Samih Shukri ya tabbatar da cewa a yayin zaman magabatan kasashen biyu za a tattauna kan yanayi da kuma rikici na kasashen Siriya, Yemen, da Libiya.

A Watanin baya-baya nan dai danganta  tayi tsami tsakanin kasashen biyu, bayan da kasar Masar ta jefa kuri'ar kin amincewa da kudirin da kasar Saudiya ta gabatar a gaban kwamitin tsaron MDD dangane da kasar Siriya, lamarin da ya sanya magabatan na Saudiya suka dakatar da sayar wa Masar din Man fetir gami da tallafin da suke bata.