Unucef Ta Samu Izinin Shiga Yankunan Da Ake Rikici A Kasar Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19740-unucef_ta_samu_izinin_shiga_yankunan_da_ake_rikici_a_kasar_sudan
Gwamnatin Sudan ta baiwa kwararru na Jami'an Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF izinin shiga yankunan da ake rikici a kasar
(last modified 2018-08-22T07:00:00+00:00 )
Apr 23, 2017 13:42 UTC
  • Unucef Ta Samu Izinin Shiga Yankunan Da Ake Rikici A Kasar Sudan

Gwamnatin Sudan ta baiwa kwararru na Jami'an Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF izinin shiga yankunan da ake rikici a kasar

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na Kasar China ya habarta cewa Ofishin kula da harakokin jin kai na MDD ya sanar a jiya Assabar cewa Gwamnatin Sudan ta baiwa kwararru na Jami'an Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF izinin shiga wasu yankuna da ake rikici tsakanin 'yan tawaye da Gwamnati domin gudanar da aiyukan jin kai, kamar  bayar da kariya ga kananen yara, bayar da ilimi, kiyon lafiya, raba abinci mai gina jiki, da kuma tsabtaceccen rusa sha da sauransu.

Kimanin shekaru biyar kenan da Gwamnatin ta Sudan ke hana Kwararru na MDD izinin shiga wasu yankuna dake ake rikci a kasar.

Tun daga shekarar 2003 ne yankin Darfur ya fada cikin rikci tsakanin Gwamnati da 'yan tawaye, yayin kuma da a shekarar 2011 jihohin Kirdufan ta Kudu da Nail-Aby suma suka fada cikin irin wannan rikici.

A wata sanarwa da ta fitar MDD ta ce daga farko soma rikicin kasar Sudan zuwa yanzu kimanin Mutane dubu 300 ne aka kashe yayin da sama da Mutane miliyan biyu da rabi suka rabu da mahalinsu.