Bam Ya Hallaka Mutane Da Dama A Arewa Maso Gabashin Somaliya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19742-bam_ya_hallaka_mutane_da_dama_a_arewa_maso_gabashin_somaliya
Akalla Mutane 8 ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin Bam a arewa maso gabashin kasar Somaliya
(last modified 2018-08-22T11:30:00+00:00 )
Apr 23, 2017 18:14 UTC
  • Bam Ya Hallaka Mutane Da Dama A Arewa Maso Gabashin Somaliya

Akalla Mutane 8 ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin Bam a arewa maso gabashin kasar Somaliya

Kamfanin dillancin Labaran Isna na kasar Iran ya nakalto Ahmad Muhamad babban jami'i a Ma'aikatar Jami'an 'yan sandar kasar Somaliya na cewa akalla Mutane 8 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 3 na daban suka samu rauni sanadiyar tashin Bam a wannan Lahadi a gefen hanyar garin Galgala na jihar Puntland dake arewa maso gabashin kasar.

Ahmad Muhamad ya kara da cewa a halin dake ciki, jami'an tsaron kasar na cikin yanayin yaki ne da mayakan kungiyar ta'addancin ta Ashabab mai alaka kut da kut da kungiyar Alka'ida.

Tuni dai kungiyar Ashabab ta dauki alhakin tashin bam din. idab ba a manta ba dai ,tun a watan Augustan Shekarar 2011 ne Jami'an tsaron kasar Somaliya tare da hadin gwiwar Dakarun tsaron kungiyar kasashen Afirka ta Amison ke yaki da kungiyar Ashabab a kasar.