Burkina Faso : Za'a Gurfanar Da Majalisar Ministoci Gaban Kotu
A Burkina faso kwatamcin majalisar ministoci guda ce zata gurfana gaban kotun kolin kasar bisa zargin amfani da karfi kan masu kin jinin mulkin koraren shugaban kasar Blaise Compaore a cikin 2014.
Kimanin tsaffin ministoci 34 ne zasu gurfana gaban kotun kolin kasar a ranar Alhamis mai zuwa, da suka hada tsohon fira ministan kasar Luc Aldophe Tiao da kuma tsaohon shugaba Blaise Compaore.
Sai dai shugaba Compaore dake gudun hijira a Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast ba zai halarci zamen kotun ba, inda lauyensa ne Pierre Olivier dan asalin kasra Faransa zai halarci zamen domin kare shi.
Ana dai zargin ministocin ne da hada kai wajen bada umurnin yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga a lokacin wani taronsu na gaggawa a ranar 29 ga watan Oktoban 2014.
A yayin taron dai majalisar ministocin ta wacen lokacin ta bukaci sojojin kasar dasu kawo karshen masu zanga-zangar dake adawa da shirin gwamnatin ta lokacin na neman gyaren fuskawa kundin tsarin mulkin kasar ta yadda kokaren shugaban kasar Compaore zai samu damar yin tazarce.
Zanga-zangar ta waccen lokacin data cilastawa shugaba Compaore tsarewa daga kasar bayan shafe shekaru 27 na mulki ta yi sanadin mutuwar mutane bakai da kuma raunana wasu 88 na daban.