Khartum Na Zargin Sudan Ta Kudu Da Ganawa Da 'Yan Tawayen Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19784-khartum_na_zargin_sudan_ta_kudu_da_ganawa_da_'yan_tawayen_sudan
Hukumar leken asiri ta kasa a Sudan ta zargi Sudan ta kudu da ganawa da 'yan tawayen dake yakar dakarun gwamnatin Khartum.
(last modified 2018-08-22T11:30:01+00:00 )
Apr 25, 2017 05:43 UTC
  • Khartum Na Zargin Sudan Ta Kudu Da Ganawa Da 'Yan Tawayen Sudan

Hukumar leken asiri ta kasa a Sudan ta zargi Sudan ta kudu da ganawa da 'yan tawayen dake yakar dakarun gwamnatin Khartum.

Hukumar ta NISS ta yi kakkaukar suka dangane da ganawar da shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Taban Deng da kuma wasu mayan jami'an soji Sudan ta Kudun sukayi da mambobin kumgiyar 'yan tawayen Sudan ta (SPLA-N).

'Yan tawayen  (SPLA-N) dai na yaki da sojojin gwamnatin Sudan a yankunan Blu Nile da kuma kudancin Kordofan.

A cewar hukumar leken asiri ta Sudan wannan haduwar na da manufar shirya wata makarkashiya da nufin tada yaki a kasar, a daidai lokacin da ita take ci gaba da karbar 'yan gudun hijira Sudan ta Kudun.

Wasu alkaluma daga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD (UNHCR) sun nuna cewa sama da 'yan sudan ta kudu 300,000 ke gudun hijira a Sudan saboda  rikicin da kasar ke fama da shi da kuma fari.