Masar Ta Hana Wani Fitaccen Dan Jarida Na Sudan Shiga Cikin Kasarta
Gwamnatin kasar Masar ta hana Tahir Sati wani fitaccen dan jarida na kasar Sudan shiga cikin kasarta, bayan da ya safka a filin jirgi na birnin Alkahira.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Masar ta hana Tahir Sati shiga cikin kasar, tare da mayar da shi cikin jirgin da ya dauko daga birnin Khartum.
Mahukuntan Masar dai ba su bayyana dalilin yin hakan ba, sai dai a nasu bangaren mahukuntan kasar Sudan sun bayyana hakan a matsayin mataki na zalunci da shiga hurumin dan kasar, wanda ya samu izinin shiga Masar a hukumance.
Kasashen Masar da Sudan dai sun samu sabani ne sakamakon goyon bayan da Sudan take baiwa kasar Habasha domin gina babbar madatsar ruwa ta Al-nahda, shirin da Masar ke gani zai kawo mata matsala matuka ta fuskar ayyukan noman rani.