Najeriya : An Kai Jerin Hare-Hare Kunan Bakin Wake A Maiduguri
Apr 26, 2017 06:43 UTC
Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu jerin hare haren kunar bakin wake uku sunyi sanadin mutuwar mutun guda da kuma raunana wasu gomman mutane a wajen Maiduguri.
Majiyoyin tsaro dana agaji sun shaidawa masu aiko da rahotanni cewa mata uku ne suka kai hare-haren a safiyar Larabar nan.
Bayanai daga yankin na cewa 'yan kunnar bakin waken sun tarwatse ne kafin suka kai inda suka doshi kai harin.
Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki biyu bayan wani harin bom da ya yi sanadin mutuwar wasu dakarun hadin gwiwa hudu a yankin.
Tags