Ana Gangamin Cika Kwanaki 500 Da Tsare Sheikh Zakzaky
-
HOTO daga shafin facebook na Al\\\\\\\'mizan
Dubban almajirai mabiya da masu tausayawa Shaikh Ibraheem Yakub Zakzaky na kungiyar 'yan uwa musulmi a Najeriya na gangami a Abuja don nuna rashin jin dadinsu da ci gaba da tsare shehun na su.
Wannan dai na zuwa ne a yayin da Malamin ya cika kwanaki 500 ana tsare da shi ba tare da wani kwakkwaran dalili ba a cewar kungiyar ta (Islamic Mouvement in Nigeria).
Mahalarta gangamin dai sun shiadawa masu aiko da rahotannin cewa, sun fito ne cikin lumana don nuna rashin yardarsu da yadda gwamnatin Shugaba Buhari take ci gaba da nun ahalin ko kula akan kisan kiyashin Zaria da sojoji suka aiwatar bisa umurnin ta.
Kungiyar ta IMN ta ce an kashe mata mabiya sama da dubu daya a cikin kasa da sa'o'i 48 a karshen watan Disamba na shekara 2015.