Rikicin Kabilanci Ya Lashe Rayukan Mutane Masu Yawa A Kasar DR Congo
Majiyar dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da ke Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta bayyana cewa: Akalla mutane 20 ne suka rasa rayukansu sakamakon bullar rikicin kabilanci a lardin Kasai da ke tsakiyar kasar ta Dimokaradiyyar Congo.
A bayanin da majiyar dakarun wanzar da zaman lafiya da sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a jiya Laraba yana dauke da bayanin cewa: Rikicin kabilanci da ya kunno kai a yankin Mungamba da ke lardin Kasai a tsakiyar kasar Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo tun daga ranar 19 ga wannan wata na Aprilu zuwa yanzu, an samu hasarar rayukan mutane akalla 20 tare da na tarin dukiyoyi.
A gefe guda kuma majiyar rundunar 'yan sandan kasar ta Dimokaradiyyar Congo ta sanar da cewa: A halin yanzu jami'an 'yan sanda sun samu nasarar shawo kan rikicin tare da gudanar da sintiri a yankin da nufin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.