Najeriya : Mutane 813 Sakarau Ya Kashe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19856-najeriya_mutane_813_sakarau_ya_kashe
A Najeriya adaddin mutanen da ciwan sankarau ya kashe ya kai 813 a cewar ma'aikatar kiwan lafiya kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:01+00:00 )
Apr 27, 2017 06:40 UTC
  • Najeriya : Mutane 813 Sakarau Ya Kashe

A Najeriya adaddin mutanen da ciwan sankarau ya kashe ya kai 813 a cewar ma'aikatar kiwan lafiya kasar.

Duk da hakan dai a cewar ministan lafiya na kasar Isaac Adewole a wani taron manema labarai a Abuja an samu ci gaba wajen rage saurin yaduwar cutar.

kawo yanzu dai an cewarsa an shiga mako na 16 da bullar cutar, kuma nan da makwani masu zuwa za'a kai ga murkushe cutar.

Cutar dai tafi shaffar jihohin Zamfara, Sokoto, Katsina, Kebbi da kuma Niger, kuma tuni aka kaddamar da gagarimin kamfe na shaushawar riga kafin cutar.