Burkina Faso : An Dage Shari'ar Compaoure Da Ministocinsa
Apr 27, 2017 11:10 UTC
A Burkina faso kotun kolin kasar tadage shari'ar koraren shugaba Blaise Compaore da kuma tsaffin ministocinsa wadanda ake zargi da kashewa da kuma azabtar da masu zanga-zangar nuna adawa da gwamnatinsu.
kotun ta dage shari'ar ne har zuwa ranar 4 ga watan Mayu.
Kimanin tsaffin ministoci 34 ne zasu gurfana gaban kotun ciki har da tsohon fira ministan kasar Luc Aldophe Tiao.
Ana dai zargin ministocin ne da hada kai wajen bada umurnin yin amfani da karfi kan masu zanga-zanga a lokacin wani taronsu na gaggawa a ranar 29 ga watan Oktoban 2014.
Zanga-zangar ta waccen lokacin ta cilastawa shugaba Compaore tsarewa daga kasar bayan shafe shekaru 27 na mulki.
Tags