Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojojin Najeriya 5
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19884-harin_kunar_bakin_wake_ya_kashe_sojojin_najeriya_5
Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojojin kasar biyar ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai masu da mota a yankin arewa maso gabashin kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Apr 28, 2017 05:34 UTC
  • Harin Kunar Bakin Wake Ya Kashe Sojojin Najeriya 5

Majiyoyin tsaro a Najeriya sun ce sojojin kasar biyar ne suka rasa rayukansu a wani harin kunar bakin wake da aka kai masu da mota a yankin arewa maso gabashin kasar.

Harin na jiya an kai shi ne kan ayarin motocin sojin kasar dake sintiri a yankin, inda kuma sojiji sama da 40 suka raunana.

Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dilnacin labaren AFP cewa maharin na Boko Haram ne bangaren Abu Mus'ab Al-Barnawi.

An dai kai harin ne jiya Alhamis kan tawagar sojojin dake aikin sarkake yankin daga barazana boko haram wandanda suke kan hanyarsu ta zuwa barikin sojin Damboa dake nisan kilomita 90 daga Maiduguri.