Kirghizstan: Zaftarewar Kasa ta Kashe Mutane 24
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19920-kirghizstan_zaftarewar_kasa_ta_kashe_mutane_24
Rahotanni daga Kirghizstan na cewa mutane 24 ne suka rasa rayukansu a yayin wata zaftarewar kasa a kauyen Ayu dans dake jihar Och a kudancin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:30:02+00:00 )
Apr 29, 2017 11:04 UTC
  • Kirghizstan: Zaftarewar Kasa ta Kashe Mutane 24

Rahotanni daga Kirghizstan na cewa mutane 24 ne suka rasa rayukansu a yayin wata zaftarewar kasa a kauyen Ayu dans dake jihar Och a kudancin kasar.

Da yake tabbatar da hakan ga kamfanin dilancin labarai na AFP ministan kasar mai kula da ayyukan gaggawa, Koubatbek Boronov ya ce tara daga mutanen yara ne.

Lamarin dai ya faru da sanyin safiyar wannan Asabar inda gidaje shida suka rufta kan mutane.

Tuni gwamnatin kasar ta bada umurnin kwashe wasu iyalai 40 dake rayuwa a kusa da kauyen da bala'in ya faru.