Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Kori Ma'aikatan Tashar Aljazeera Daga Kasar
Hukumar da ke kula da kafofin yada labarai a kasar Sudan ta kudu, ta sanar da korar ma'aikatan tashar Aljazeera mallakin gwamnatin kasar Qatar, saboda yada rahotanni na karya a kan kasar.
Kamfanin dillancin labaran Irna ya bayar da rahoton cewa, babban daraktan hukumar kula da kafofin yada ta kasar Sudan ta kudu Lija Alir Kwaye ya sanar a daren jiya cewa, sun dakatar da dukkan ayyukan ma'aikatan tashar Aljazeera na bangaren turanci a kasar, sakamakon gudanar da aiki da ya saba wa aikin jarida.
Alira ya ce, tashar Aljazeera ta bayar da rahotanni da suke kara azuzuta wutar rikici a cikin kasar domin cimma wasu manufofi na siyasa, wanda hakan ke yin sanadiyyar mutuwar mutane, wannda hakan a cewarsa ya sabawa kaida ta aikin jarida,a kan haka gwamnatin Sudan ta kudu dauki matakin da ya dace a kan ma'aikatan wanann tasha a cikin kasarta.