Karfafa Harkokin Samar Da Abincin Halal A Kasar Kenya
Gwamnatin kasar ta sanar da cewa tana shirin kara karfafa harkokin samar da abincin halal a cikin kasarta.
Ministan kula da harkokin yawon bude na kasar Kenya ne ya sanar da hakan a lokacin da yake ganawa da jami'an huldar diflomasiyya na kasar Iran a kasar ta Kenya.
Ministan ya ce wanann tsari zai kasance ne bisa kaidoji na addinin muslunci wajen samar da irin wadannan kayayyaki, bisa la'akari da cewa kasar Kenya kasa ce mai karbar baki a kowane lokaci daga kasashen duniya daban-daban.
Ya ce daga cikin bakin da suke zuwa Kenya akwai musulmi daga kasashen larabawa da sauransu, wadanda sukan bukaci abincin halal tsawon lokacin da zamansu a kasar, kuma rashin samun wadataccen kayayyakin halal a kasar zai kawo nakasu matuka wajen kasa gamsar da baki musulmi.
A kan haka ya jaddada cewa kasashen Kenya da Iran za su yi aiki kafada da kafada wajen samar da irin wadannan kayayyaki a cikin kasar, duk kuwa da cewa tuni an riga an fara shirin, kuma an fara ganin amfaninsa matuka.