An Kama Wasu Sojoji Biyu Bisa Zargin Kashe Matashin Ministan Kasar Somaliya
Gwamnatin kasar Somaliya ta sanar da kame wasu sojoji guda biyu a jiya Alhamis bisa zargin suna da hannu cikin kisan gillan da aka yi wa ministan ayyuka na kasar Abbas Abdullah Sheikh Siraji a shekaran jiya Laraba.
Yayin da yake tabbatar da hakan, mataimakin babban mai shigar da kara a kotun soji ta kasar Somaliyan Mumin Husein Abdullahi ya ce a halin yanzu ana tsare da wasu sojoji masu gadin babban mai bincike na kasar a gidan yarin Mogadishu saboda zargin da ake da shi na cewa suna da hannu cikin kisan da aka yi wa ministan.
A shekaran jiya Laraba ce dai Minista Abbas Abdullahi Sheikh Siraji, wanda shi ne minista mafi karancin shekaru a gwamnatin Somaliyan, ya rasu a cikin motarsa lokacin da wasu jami'an tsaro da suke sintiri suka bude wa motar tasa wuta a kusa da fadar shugaban kasar, a birnin Mogadishu bisa zaton cewa 'yan ta'addan kungiyar Al-Shabab ne a cikin motar.
Shugaban kasar Somaliyan Mohamed Abdullahi Mohamed Farmajo ya sanar da cewa ya umarci shugabannin jami'an tsaro,da su yi duk abin da za su iya wajen kawo karshen irin wannan hali na rashin tsaro da kasar take fuskanta su gudanar da bincike don gano wadanda suka aikata wannan aikin.