Sudan: An saki dan kasar Faransan da aka yi garkuwa da shi.
May 07, 2017 07:40 UTC
Hukumar tsaron kasar Sudan ta ce an saki dan kasar Faransan da aka yi garkuwa da shi a yankin Darfur.
Hukumar tsaron kasar Sudan ta ce an saki dan kasar Faransan da aka yi garkuwa da shi a yankin Darfur.
Dan kasar Faransan wanda ba a bayyana ko wane ne shi ne ba,an sace shi ne a kasar Chadi a yankin tono ma'adanai na Abeche, mai nsian kilo mita 800 daga birnin N'Djamena, kafin daga baya a shigar da shi cikin kasar Sudan, zuwa yankin Darfur.
Kasar Sudan ta yi aiki tare da kasashen Chadi da kuma Faransa wajen kokarin sako da mutumin.
Tags