MDD: Yara Kimanin Miliyan 2 Sun Bar Gidajensu A Sudan Ta Kudu
Majalisar dinkin duniya ta sanar da cewa sakamakon yaki da yunwa kimanin yara miliyan biyu sun bar muhallansu a cikin kasar Sudan ta kudu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya habarta cewa, a daren jiya kwamitin kula da 'yan gudun hijira na majalisar dinkin ya fitar da wani bayani dangane da halin da ake ciki a kasar Sudan ta kudu, in bayanin ya tabbatar da cewa lamurra suna ci gaba da kara tabarbarewa a kasar, sakamakon yaki da yunwa.
Bayanin ya ce a halin yanzu batun 'yan gudun hijira a cikin kasar Sudan ta kudu na daga cikin lamurra da suka fi daga wa jami'an hukumar hankali, musamman idan aka yi la'akari da yadda matsalar take shafar mata da kananan yara kai tsaye.
Rikicin kasar Sudan ta kudu ya balle ne tun bayan da shugaban kasar Salva Kiir ya safke mataimakinsa Reick Machar a karshen shekara ta 2013.