Nijar : Isufu Ya Taya Sabon Shugaban Faransa Murna
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20236-nijar_isufu_ya_taya_sabon_shugaban_faransa_murna
Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar ya taya sabon shugaban kasar faransa Emanuelle Macron murna akan nasara lashe zaben shugabancin kasar.
(last modified 2018-08-22T07:00:05+00:00 )
May 10, 2017 01:19 UTC
  • Nijar : Isufu Ya Taya Sabon Shugaban Faransa Murna

Shugaba Isufu Mahamadu na Jamhuriya Nijar ya taya sabon shugaban kasar faransa Emanuelle Macron murna akan nasara lashe zaben shugabancin kasar.

Wata sanarwa daga fadar shugaban kasar da shafin yada labarai na Actuniger ya wallafa ta ce shugaba Isufu ya aike da sakon taya Macron murna akan nasara da ya samu da gagarimin rinjaye a zaben faransa na ranar 7 ga watan Mayu.

Sanarwar ta ce al'ummar faransa a galibinsu sun baka yarda ta hanyar zaben ka a matsayin shugaba na takwas a karkashin jamhuriya ta biyar ta faransa.

Shugaba Isufu ya yi fatan hakan zai bude wani sabon babi na kara inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.

Nijar da faransa dai na da dadaddiyar hulda data shafi cinikin uremium da kuma tsaro, bayan kasancewar Faransar ce tayiwa kasar mulkin mallaka.