An Sallami Babban Hafsan Sojan Sudan Ta Kudu
Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir ya sallami dadadden babban Hafsan Sojojin Kasar Paul Malong.
Babu dai wani bayani kan dalilin sallamar Malong din, kuma ba'a san ko za a nada Malong kan wani mukami na dabam ba.
Wannan ya biyo bayan ajiye aiki da Janar-Janar da dama su ka yi, wadanda su ka yi zargin cewa Sojojin Sudan Ta Kudu sun aikata kisan kare dangi da kuma laifukan yaki.
Tuni dai shugaban kasar ya nada James Ajong a matsayin sabon babban Hafsan sojin kasar.
Sudan Ta Kudu ta shiga rudani ne ne tun bayan da aka shiga takun saka tsakanin Kiir dan Kabilar Dinka da Mataimakinsa, Riek Machar, dan Kabilar Nuer a cikin shekara 2013.
Wannan gwagwarmaya ta rikide zuwa yaki gadan-gadan a Juba babban birnin kasar, wanda nan da nan ya wanzu zuwa sassan Kasar, wanda ya haddasa karancin abinci a sassan kasar da tilasta mutane a kalla miliyan 3 barin gidajensu.