An Cafke Mambobin Kungiyar (Daesh) ISIS A Morocco
jami'an tsaron kasar Morocco sun samu nasarar damke wasu daga cikin mambobin kungiyar 'yan ta'adda ta Daesh a kasar.
Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya nakalto daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Morocco cewa, rundunar yaki da ta'addanci ta kasar ta cafke mutane 6 mambobin kungiyar Daesh, wadanda suke da kwarewa a wajen hada bama-bamai, da kuma tayar da su, bayan samun horo daga wasu 'yan ta'adda tafkfiriyya da ke yaki a kasashen Syria da Iraki.
Bayanin ya ce mutanen suna cikin shirin kaddamar wasu munanan hare-haren bama-bamai a wasu muhimamn wurare a cikin kasar ta Morocco.
A cikin shekara ta 2016, jami'an tsaron Morocco sun sanar da kame 'yan ta'addan wahabiyya takfiriyya 273 a kasar, da suke da alaka da kungiyar ISIS.