An Kafa Gwamnatin Hadin Kan Kasa A Kasar Sudan
Gwamnatin Kasar Sudan ta bada sanarwan kafa sabuwar gwamnarin wacce ta kari gawamnatin hadin kan kasa
Tashar television ts sky news ta bayyana cewa shugaban umar hassan al-bashir ya nada Hasbu Muhammad abdurrahman a matsayin mataimakin shugaban kasa, kuma a yau jumma'a ce ake saran sabuwar majalisar ministocin kasar zata yi rantsuwar kama aiki.
Majiyar ta kara da cewa Mohammad Hassan almirgani shi ne aka nada a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko, sai kuma Ibrahim Mahmood Hamid, Musa Muhammad Ahmad , Abdurrahman Sadikul Mahdi duk an nada su ne a matsayin masu bawa shugaban kasa shawara.
Banda haka shugaba Albashir ya nada Bakri Hassan Saleh a kan kujerar Priminista, kuma kafin haka shi ne mataimakin shugaban kasa na farko.
Shugaban Umar ya bayyana cewa gwamnatin hadin kan kasa da kuma jami'anta da ya dana duk sun cancanci mukaman da aka basu, sai dai Priministan ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar har yamzu bata amince da ministoci guda 6 ba