Najeriya: Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Tarwatsa Kansu A Jami'ar Maiduguri
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20342-najeriya_wasu_'yan_kunar_bakin_wake_sun_tarwatsa_kansu_a_jami'ar_maiduguri
Wasu 'yan kunar bakin bake su uku da ake sa ran 'yan Boko Haram ne sun tarwatsa kansu a lokacin da suke shirin kutsa kai a cikin bangaren ayyuka na jami'ar Maiduguri
(last modified 2018-08-22T11:30:06+00:00 )
May 13, 2017 12:46 UTC
  • Najeriya: Wasu 'Yan Kunar Bakin Wake Sun Tarwatsa Kansu A Jami'ar Maiduguri

Wasu 'yan kunar bakin bake su uku da ake sa ran 'yan Boko Haram ne sun tarwatsa kansu a lokacin da suke shirin kutsa kai a cikin bangaren ayyuka na jami'ar Maiduguri

Rahotanni daga birnin na Maiduguri da ke Jahar Borno a tarayyar Najeriya na cewa, maharan sun yi yunkurin kai harin ne da jijjifin safiyar yau Asabar, amma ba su samu nasarar shiga bangaren da suka yi nufi ba, dukkanin maharan uku sun mutu tare da mai gadin wurin.

A daya bangaren kuma wasu daga cikin kwamandojin kungiyar ta Boko Haram da aka musayar 'yan matan Chibok 82 da su, sun bayyana a cikin wani fafan bidiyo dauke da bindogogi,  inda wani daga cikinsu mai suna Shu'abu Moni yake yin magana da kuma yin barazanar za su kai hare-hare a cikin birnin Abuja, da kuma kan mutanen gari matukar dai ba su daina shirka ba a cewarsa.