Sakamakon Wani Bincike: Musulunci Na Yaduwa A Kasar Zimbabwe
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20404-sakamakon_wani_bincike_musulunci_na_yaduwa_a_kasar_zimbabwe
Sakamakon wani bincike ya nuna cewa kasar Zimbabwe na daga cikin kasashen Afirka mabiya addinin kiristanci da muslunci ke kutsawa a cikin al'ummar kasar.
(last modified 2018-08-22T11:30:07+00:00 )
May 15, 2017 12:29 UTC
  • Sakamakon Wani Bincike: Musulunci Na Yaduwa A Kasar Zimbabwe

Sakamakon wani bincike ya nuna cewa kasar Zimbabwe na daga cikin kasashen Afirka mabiya addinin kiristanci da muslunci ke kutsawa a cikin al'ummar kasar.

Binciken wanda bangaren nazari kan halaye da kuma zamantakewar jama'a na jami'ar Harare ya gudanar, ya tabbatar da cewa addinin muslucni shi ne addinin da ya samu kutsawa a cikin al'ummar kasar Zimbabwe masu tsananin riko da addinin kiristanci.

Bayanin ya ce bisa la'akari da cewa kasar Zimbabwe da ke kudancin Afirka, na daga cikin kasashen nahiyar Afirka da suke bin addinin kiristanci, a  cikin shekarun baya-bayanan addinin muslunci yana samun shiga a lunguna na kasar, inda a halin yanzu su ne kashi uku cikin dari na al'ummar kasar, wadda a 'yan shekarun baya babu musulmi a cikintsu.

Binciken ya nuna cewa, daga cikin dalilan da suka sanya muslunci ya samu shiga a cikin al'ummar Zimbabwe, har da yadda al'ummar kasar suke da kokarin karatu da kuma bincike, baya ga haka kuma suna mu'amala da al'ummomin duniya daban-daban.