Ana Ci Gaba Da Zaman Dar-Dar A Sudan Ta Kudu
Kimanin Sojoji 4 ne suka rasa rayukansu sanadiyar wani hari da 'yan tawaye suka kai kudancin kasar Sudan ta kudu
Hukumar gidan telbijin da Radio na kasar Iran ya nakalto David Lukanga Gwamnan jihar Nahar Yaay dake kudancin kasar Sudan ta kudu na cewa akalla Sojoji 4 ne suka hallaka yayin da wasu 6 na daban suka jikkata sanadiyar wani mumunan hari da 'yan tawaye suka kaiwa garin Yaay.dake kusa da kan iyakar kasar da kasashen Uganda da Jumhoriyar Demokaradiyar Congo.
Mista David Lukanga ya bukaci Al'ummar garin da su fice daga cikinsa domin kauracewa mumunan hare-haren 'yan tawaye a nan gaba,sannan kuma ya bayyana cewa 'yan tawayen na son rusa garin na Yaay ne tare kuma da muzgunawa fararen hula.
Tun bayan da Shugaba Salva Keir ya sauke mataimakinsa Riek Machar, kasar Sudan ta kudu ta fada cikin rikici tsakanin Sojojin dake biyayya da Shugaba Keir da kuma na koraren mataimakin Shugaban kasar kuma madugun 'yan tawaye Riek Machar. duk da cewa an cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta a shekarar 2015, amma har yanzu kasar na ci gasba da fuskantar rikici.