Nijar / Ta'addanci : An Rufe Wasu Kasuwanni Da Takaita Zirga-zirga Ababen Hawa
Hukumomi a yankunan dake yammaci a Nijar sun sanar da fara aiki da wata doka data tanadi takaita zirga-zirga ababen hawa da kuma rufe wasu kasuwanni saboda barazanar yan ta'adda dake shigowa kasar daga Mali.
Dokar dai ta shafi yankuna da dama dake jihohin Tillaberi da kuma Tawa, karkashin dokar ta bakin da gwamnatin kasar ta tsawaita a watan Maris da watanni uku saboda yawaitar kai hare-hare a yankunan dake iyaka da makofciyyar kasar Mali.
Matakin dai ya shafi takaita zirga-zirga ta duk ababen hawa a kauyukan dake fama da matsalar daga karfe takwas na dare ogogo wurin wato bakwai na GMT har zuwa shida da rabi na safe, a yayin da kuma aka rufe kasuwannin kauye 16.
Wani jami'in yankin ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa 'yan ta'addan na amfani da ababen hawan musamen babur domin tafiyar da harkokinsu ciki har da saye-saye a cikin kasuwannin da kuma samun bayyanai daga mutanensu.
Wasu alkaluma na MDD sun nuna cewa an kai hare-hare har sau 34 a jihohin Tawa da Tillaberi daga watan fabrairu na shekara 2016.