Kasashen Tanzaniya Da Uganda Sun Bukaci EU Ta Cirewa Burundi Takunkumi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20608-kasashen_tanzaniya_da_uganda_sun_bukaci_eu_ta_cirewa_burundi_takunkumi
Shugabannin kasashen Tanzaniya da Uganda sun mika kira ga kungiyar tarayya Turai data dage takunkumanta ga kasar Burundi.
(last modified 2018-08-22T07:00:08+00:00 )
May 22, 2017 08:49 UTC
  • Kasashen Tanzaniya Da Uganda Sun Bukaci EU Ta Cirewa Burundi Takunkumi

Shugabannin kasashen Tanzaniya da Uganda sun mika kira ga kungiyar tarayya Turai data dage takunkumanta ga kasar Burundi.

Bangarorin sun bayyana hakan ne a yayin wani taron kasashen yankin a birnin Dar es Salam a karshen makon Jiya.

Saidai tuni wani jami'in diflomatsiya kungiyar ta EU ya yi watsi da Kiran na shugaba Yoweri Museveni na Uganada da takwaransa na Tanzaniya John Magufuli. 

Shugaban Museveni wanda shi ne ke rike da shugabancin karba karba na kungiyar ta EAC ya ce suna bukatar duk irin matakin da EU za ta daukan a kan kasashen dake zama mamba a cikinta to yana da kyau su tattauna kan batun tukuna. 

Saidai jakadan kungiyar tarayya turai a kungiyar, Roeland van de Geer ya ce takunkuman kungiyar kan Burundi suna nan daram.