Libya: Gargadi Akan Yiyuwar Shigar 'Yan ta'adda Cikin Kasar Libya Daga Waje
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i20616
Gwamnatin Libya ta sanar da cewa da dama daga cikin kwamandojin 'an ta'adda suna shigar kasar ne daga waje.
(last modified 2018-08-22T11:30:08+00:00 )
May 22, 2017 19:14 UTC
  • Libya: Gargadi Akan Yiyuwar Shigar 'Yan ta'adda Cikin Kasar Libya Daga Waje

Gwamnatin Libya ta sanar da cewa da dama daga cikin kwamandojin 'an ta'adda suna shigar kasar ne daga waje.

Gwamnatin Libya ta sanar da cewa da dama daga cikin kwamandojin 'an ta'adda suna shigar kasar ne daga waje.

Kamfanin Dillancin Labarun Xinhua na kasar Sin, ya ambato shugaban majalsiar shugabancin gwamnatin hadin kan kasa, Fa'iz al-Siraj yana cewa; Mafi yawancin 'yan ta'adda da kwamandojojinsu suna shiga cikin kasar ne daga waje, don haka nauyi yana wuyan kasashen makwabta.

Al-siraj ya ci gaba da cewa; 'Yan ta'addar suna amfani da rashin tsaron da ake da shi da kuma kwararar 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba.

Al-siraj ya kuma cewa; Wajibi ne ga kungiyoyin kasa da kasa su taimakawa kasar ta Libya a yakin da ta ke yi da 'yan ta'adda.

Shugaban majalisar shugabancin kasar ta Libya, ya kuma ce; Kasar tana yin nasara a yakin da ta ke yi da 'ta'addanci saboda al'ummar kasar sun shiga ana yi da su, haka nan kuma wasu kasashe.